An Shiga Tashin Hankali a Jigawa: Kwale Kwale Ya yi Hatsari da Mutum 20, An Rasa Rayuka

  • Rahoto ya nuna cewa wani kwale-kwale dauke da mutane 20 ya yi hatsarin yayin tsallaka kogin Gamoda da ke a Taura, jihar Jigawa
  • Rundunar 'yan sandan Jigawa da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce mutane biyar sun mutu yayin da wasu 15 suka bace a hatsarin
  • Daga cikin wadanda suka mutu akwai yaro dan shekara 15 da kuma dattijo dan shekara 75 yayin da ya kasance maza ne duka biyar din

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - An tabbatar da mutuwar mutane biyar tare da bacewar wasu 15 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a kogin Gamoda da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

NNPC ke yiwa tattalin arziki zagon kasa? Kyari ya wanke kamfanin Najeriya

Hadarin ya afku ne a kauyen Nahuce a ranar Alhamis lokacin da fasinjojin jirgin ke kokarin tsallaka kogin bayan dawowa daga kasuwa.

Kwale-kwale ya yi hatsarin da mutum 20

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shisu ya ce fasinjoji 20 ne a cikin kwale-kwalen lokacin da hatsarin ya afku, inji rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A yau (Alhamis), 08 ga Agusta, 2024 da misalin karfe 12:00 na rana, kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji 20 a kogin Gamoda a kauyen Nahuce a karamar hukumar Taura ya kife.“Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda tare da hadin gwiwar masu aikin 'su' da wasu bayin Allah sun yi tururuwa zuwa wurin domin gudanar da aikin ceto.“Abin takaici, biyar biyar daga cikin fasinjojin sun mutu.”

- Inji DSP Lawan.

Kara karanta wannan

Ana zanga zanga, yan bindiga sun kashe mutane, an yi garkuwa da wasu rututu a Arewa

Ana kokarin ceto mutum 15

Ya bayyana sunayen wadanda suka mutu da: “Abdurra’uf Mohd (15), Suleman Ali (20), Shafiu Mohd (25), Ado Nafance (75) da Alasan Mohd (16) duka daga karamar Taura."

Jaridar Vanguard ta ruwaito kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin ceto sauran fasinjoji 15 da aka bayyana bacewarsu.

Kakakin rundunar ya mika sakon ta’aziyyar kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP A.T. Abdullahi ga iyalan wadanda suka rasu.

Kwale-kwale ya kife da 'yan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu kifewar kwale kwale da wasu yan kasuwa a jihar Jigawa da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa kifewar kwale kwalen ya jawo hasarar ran wata mata yayin da hatsarin ya rutsa da mutum 20.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYRxfZhmq5qrmJ67brTAp6KapJlirm62yKCYsJldn7azs8inZKutp5Z6uq2MsqBmoJGpwKK%2ByGabmmWdqsG2uYxqbGg%3D